Kasar Rasha Ta Ce Canjin Gwamnati A Amurka Ba Zai Kawo Karshen Yakin Ukraine Ba

Gwamnatin Rasha ta bayyana cewa: Idan Donald Trump ya yi ƙoƙarin dakatar da yakin Ukraine, to za a kashe shi Mataimakin shugaban kwamitin tsaron kasar

Gwamnatin Rasha ta bayyana cewa: Idan Donald Trump ya yi ƙoƙarin dakatar da yakin Ukraine, to za a kashe shi

Mataimakin shugaban kwamitin tsaron kasar Rasha Dmitry Medvedev, ya yi furuci da cewa: Dan takarar shugabancin Amurka na jam’iyyar Republican, Donald Trump, ba zai iya dakatar da rikicin Ukraine ba bayan nasarar darewarsa kan karagar shugabancin Amurka, kuma idan ya yi ƙoƙari kawo karshen rikicin, za a iya kashe shi.

A cikin wata sanarwa da ya fitar Dmitry Medvedev ya yi nuni da cewa: Kwanaki biyu gabanin zaben shugaban kasar Amurka, babu wani dalili da zai sa Rasha ta yi wani kyakkyawan fata game da wannan zabe.

Ya jaddada cewa: “Ga Rasha, wadannan zabukan ba za su canza komai ba, domin matsayin ‘yan takarar ya nuna cikakken ra’ayin da bangarorin biyu suka amince da shi kan bukatar rashin nasarar kasar Rasha.”

Medvedev ya bayyana ‘yar takarar jam’iyyar Democrat Kamala Harris a matsayin “wawiya”, maras kwarewa kuma maras cin gashin kanta, kuma mai jin tsoron wadanda suke kewaye da ita, sannan idan ta yi nasara a zaben wadanda suke kewaye da ita ne na manyan ministoci da mataimaka, baya ga Obama da dangi na bayan fage.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments