Ministan harkokin wajen Iran Abbas Arakci ya yabi kasar Aljeriya saboda amincewar da ta yi na gabatar da zaman musamman na kwamitin tsaro akan harin wuce gona da iri da HKI ta kawo wa Iran.
A ranar Lahadin da ta gabata ne dai kwamitin tsaron ya yi zama na musamman bisa cikakken goyon bayan Aljeriya, China da kuma Rasha a suke mambobi a wannan kwamitin.
Jakadan kasar Aljeriya a Majalisar Dinkin Duniya, Ammar Bin Jami ya bayyana cewa, harin na Isra’ila akan Iran, yana cin karo sulhu da zaman lafiya na kasa da kasa.
A ranar Asabar 26 ga watan Oktoba ne dai HKI ta kawo wa Iran hari akan sansanonin soja a Tehran, Khuzistan, da Ilam. Na’urorin kariya na Iran sun kakkabo mafi yawancin makaman na ‘yan sahayoniya.
A jiya Alhamis ne dai ministan harkokin wajen na Iran ya tattauna ta wayar tarho da takwaransa na Aljeriya, Ahmad Attaf, inda ya yaba wa kasarsa akan yadda take bai wa Falasdinawa kariya akan wuce gona da irin HKI da take yi musu kisan kiyashi a kowace rana.
Jamhuriyar musulunci ta Iran da kasar Aljeriya suna cikin masu yin kira da a kawo karshen kisan da HKI take yi wa al’ummar Falasdinu a kowace rana.