Shugaban kungiyar Ansarullah na kasar Yemen ya bayyana cewa; Yamen a shirye take ta fuskanci kowane irin mataki da Amruka da Isra’ila za su dauka akanta.
Sayyid Abdulmalik Al-Husi wanda ya gabatar da jawabi a yau Alhamis dangane da abubuwan da suke faruwa a Falasdinu da Lebanon da kuma yammacin Asiya, ya ce; Yamen za ta cigaba da taimakawa Gaza, ba kuma za ta mika kai ba, komai girman matsin lambar da Amurka da Birtaniya da Isra’ila za ta yi mata.
Da yake Magana akan shahadar Yahya Sinwar shugaban Hamas, sayyid Abdulmalik Al-Husi ya kara da cewa; Shahadarsa tana a matsayin nasara ce dawwamammiya domin jaruntarsa za ta cusawa wasu yin gwgawarmaya.
Har ila yau, Sayyid Husi ya jinjinawa dakarun “Kassam” wacce take yi wa sojojin mamayar Isra’ila dauki daidai,kuma shahadar Yahya Sinwar ba ta kashe mata gwiwa ba, ta ma kara mata azama ne.
Da yake Magana akan Fagen dagar Lebanon kuwa, Sayyid Husi ya ce; Hare-haren da Hizbullah take kai wa,sun mayar da garin Haifa ya zama kango,sannan kuma mafi yawancin ‘yan share wuri zauna suna rayuwa ne a cikin dakunan karkashin kasa na buya.