A yammacin wannan Laraba ne sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar da wani hari ta sama a kan ofishin Al Mayadeen da ke birnin Beirut. Tashar ta kaurace wa wuraren nata a lokacin da aka fara kai hare-hare kan Lebanon.
A martanin da ta mayar, Al Mayadeen ta bayyana cewa, harin an Isra’ila yana da alaka ne da yadda tashar take bayar da sahhihan bayanai kan irin ta’asa da kuma ta’addancin da Isra’ila tajke aikatawa a kan al’ummomin Gaza da Lebanon ne.
Bayan kai harin, kusa a Hamas Mahmoud al-Mardawi ya yi Allah wadai da harin da aka kai a ofishin Al Mayadeen, yana mai bayyana aikin farko na tashar wajen bankado gaskiyar lamarin.
A wata hira da ya yi da tashar talabijin ta Al Mayadeen, al-Mardawi ya bayyana cewa, tashar ta wargaza labarai wadanda ke da alaka da Isra’ila , tare da tabbatar da matsayinta na wata kafar yada labarai da ke yaki da zalunci da mamaya da babakere na ‘yan mulkin mallakka da yahudawan sahyuniya, ta hanyar bayyana gaskiya ba tare da wani shayi ba.
A cewar ma’aikatar lafiya ta kasar Labanon, an kashe mutum guda tare da jikkata wasu biyar ciki har da wani yaro a harin da Isra’ila ta kai.
A ranar 11 ga watan Agusta ne gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta amince da kudirin da ministan sadarwa Shlomo Karhi ya gabatar na sabunta dokar hana yada labaran Al Mayadeen a cikin garuruwan Falastinawa da ke karkashin ikon Isra’ila, Matakin dai ya hada da kwace kayan aikin su da kuma toshe kafofi na yanar gizon sa.