Pezeshkian: Takunkuman Amurka da na kasashen Yamma suna hana zaman lafiya a yankin

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Amurka da kasashen yammacin Turai da gwamnatin Isra’ila na hana wanzar da zaman lafiya a yammacin Asiya. “Muna

Shugaban kasar Iran Masoud Pezeshkian ya ce Amurka da kasashen yammacin Turai da gwamnatin Isra’ila na hana wanzar da zaman lafiya a yammacin Asiya.

“Muna neman zaman lafiya da kwanciyar hankali amma kasashen yamma da Amurka, ta hanyar takunkumi, da taimaka ma gwamnatin sahyoniyawa a yake-yaken da ta bude da zubar da jini, suna hana samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin,” in ji Pezeshkian a wata ganawa da takwaransa na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, a  gefen taron kasashen BRICS a birnin Kazan na kasar Rasha a wannan Laraba.

Ya kara da cewa Amurka da wasu kasashen yammacin turai suna daukar salon siyasa mai harshen damo don bayyana wadanda ake zalunta da wadanda ba su ji ba ba su gani ba, wadanda ke neman hakkinsu a matsayin ‘yan ta’adda.

Shugaban na Iran ya jaddada cewa, a halin yanzu duniya tana fuskantar gurbatattun fassarori kan ma’anar hakkokin bil’adama da laifuffuka, yana mai cewa: karuwar tasirin BRICS da huldar mu na iya gyara dangantakar rashin adalci a duniya.

Ya kuma bayyana fatansa na cewa kasancewar Iran a cikin kungiyar BRICS zai iya taimakawa wajen rage tasirin rashin hadin kai da kuma takunkumin zalunci da Amurka da ‘yan korenta suke kakaba wa kasashe masu ‘yancin siyasa.

A wani bangare na jawabin nasa, Pezeshkian ya kuma jinjinawa marigayi shugaban kasar Afirka ta Kudu, Nelson Mandela kan yaki da rashin adalci da zalunci.

Ya ce rashin nuna son kai na Afirka ta Kudu kan abubuwan da ke faruwa a gabas ta tsakiya, da yakin da gwamnatin Isra’ila ke yi a Gaza, na nuni da kokarin Mandela na neman daidaito a tsakanin al’ummomin duniya.

A nasa bangaren shugaban na Afirka ta Kudu ya ce kasancewar Iran a cikin kungiyar BRICS zai inganta kungiyar kasashe masu tasowa.

Ya kara da cewa, kasashe mambobin BRICS suna neman ci gaban dukkan kasashen duniya, suna adawa da danne kasashe masu rauni da kuma masu tasowa don cimma muradun wasu ‘yan tsiraru a duniya.

Ramaphosa ya ce, kasashen yamma sun yi tunanin cewa kungiyar za ta ruguje  ba da jimawa ba, amma tana ci gaba cikin sauri sabanin nazarinsu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments