Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Ya Bayyana Irin Mummunan Halin Da Falasdinawa Suke Ciki

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce; Falasdinawa da ke yankin arewacin Gaza suna daf da rasa duk wata hanya ta rayuwa Babban sakataren Majalisar

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya ya ce; Falasdinawa da ke yankin arewacin Gaza suna daf da rasa duk wata hanya ta rayuwa

Babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya António Guterres ya bayyana cewa: Al’ummar yankin arewacin Zirin Gaza na fama da ci gaba da fuskantar hare-haren gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila, da killacewa da kuma fuskantar karewar duk wani kayan agajin gaggawa ta duk wata hanyar rayuwa.

Guterres ya yi gargadin cewa: Dole ne a bai wa fararen hular Falasdinu kariya tare da ba su damar samun taimako kamar yadda dokar jin kai ta kasa da kasa ta tanada.

A baya Guterres yayi nuni da cewa: Sakamakon sabon rahoton na Majalisar Dinkin Duniya na wucin gadi na tsaron abinci ya kasance “babban abin damuwa.”

Babban sakataren ya yi bayanin cewa: Bala’in yunwa da hadarin watsuwar yunwar a Gaza sakamakon takunkumin da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta kakaba wa shigar da kayan agajin dan Adam da tashin farashin kayayyakin bukatu da tsananin yadda Falasdinawa suke gudun hijira abu ne da ba za a amince da shi ba.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments