Sabuwar Na’urar Kakkabo Makamai Da Amurka Ta Sanya A Isra’ila Bai Hana Sojojin Yemen Kai Hari Tel Aviv Ba

Rundunar sojin kasar Yemen ta sake sabunta shirinta na kaddamar da hare-hare kan birnin Tel Aviv bayan yahudawan sahayoniyya sun kafa wasu sabbin na’urorin kakkabo

Rundunar sojin kasar Yemen ta sake sabunta shirinta na kaddamar da hare-hare kan birnin Tel Aviv bayan yahudawan sahayoniyya sun kafa wasu sabbin na’urorin kakkabo makamai masu linzami

Sojojin Yemen sun samu nasarar kai hari a wani sansanin sojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke gabashin birnin Tel Aviv, kakakin rundunar sojin Yemen Birgediya Janar Yahya Sari’e bayyana cewa: An kai harin ne da makami mai linzami kirar Falasdinu 2.

A wani sabon sauyi na inganta makaman kasar Yemen, sojojin kasar ta Yemen sun yi nasarar kai hari kan sansanin soji da ke gabashin birnin Tel Aviv, a farmakin farko na Yemen bayan sun auna wani sansanin sojin yahudawan sahayoniyya, duk da matakin da rundunar sojin yahudawan sahayoniyya suka dauka na kafa na’urar kakkabo makamai masu linzami samfurin THAAD na Amurka a cikin hamadar Negev a kwanakin baya.

Sabon farmakin ya zo ne bayan barazanar da Amurka ta yi wa kasar Yemen na fara kai hare-hare kan sassan kasar ta Yemen, kuma a daidai lokacin da majiyoyin haramtacciyar kasar Isra’ila suka sanar da cewa, A baya-bayan nan da aka fallasa labarin wani hari da kasar Yemen ta kai ta hanyar amfani da gungun jiragen sama marasa matuka ciki kan sassan haramtacciyar kasar Isra’ila duk da kafa na’urar kakkabo jirage da makamai masu linzami da Amurka ta kafa a Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments