Shugabannin Kasashen Somaliya Da Djibouti Sun Tattauna Shirin Kungiyar Tarayya Afirka Kan Somaliya

Shugabannin kasashen Somaliya da Djibouti sun tattauna kan makomar tawagar Tarayyar Afirka a Somaliya Shugaban kasar Djibouti Isma’il Omar Guelleh ya tattauna da takwaransa na

Shugabannin kasashen Somaliya da Djibouti sun tattauna kan makomar tawagar Tarayyar Afirka a Somaliya

Shugaban kasar Djibouti Isma’il Omar Guelleh ya tattauna da takwaransa na Somaliya Hassan Sheikh Mohamud, game da rawar da dakarun Tarayyar Afirka ke takawa wajen samar da zaman lafiya a Somaliya, da kuma hanyoyin tabbatar da mika jagorancin wanzar da kwanciyar hankali ga sabon shirin samar da zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika a kasar.

Shugaban na Somaliya ya isa Djibouti babban birnin kasar, a wata ziyarar kwana guda, a wani rangadin da ya ke yi a kasashen da ke ba da gudunmawa ga rundunar Tarayyar Afirka a Somaliya, yayin da Djibouti ke ba da gudummawar sojoji da ‘yan sanda a sabon shirin na Afirka.

Shugabannin kasashen biyu sun jaddada muhimmancin karfafa karfin jami’an tsaron kasar Somaliya don tabbatar da nasarar shirin bunkasa harkokin tsaro, inda suka jaddada bukatar mutunta ‘yancin kai da yankin kasar Somaliya, kamar yadda suka yi kirabangaren kasa da kasa da su tallafawa Tawagar Tarayyar Afirka, wacce za ta fara aikinta a watan Janairu mai zuwa, don tabbatar da samun kwanciyar hankali a Somaliya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments