Masana: Kisan Sinwar Ba Zai Kawo Karshen Kungiyar Hamas Ba

Wani bayahude mai sharhi kuma kwararre kan al’amuran Hamas, Guy Aviad, ya yarda cewa “Kungiyar Hamas za ta sake kafa karfinta tare da kwararrun mutane

Wani bayahude mai sharhi kuma kwararre kan al’amuran Hamas, Guy Aviad, ya yarda cewa “Kungiyar Hamas za ta sake kafa karfinta tare da kwararrun mutane bayan kisan Sinwar da ma wasu jagororinta.”

Ya jaddada cewa “Sinwar babban jami’i ne, amma soja ne a wannan dogon yakin da aka yi tsakanin Isra’ila da Falasdinawa, yakin da aka shafe shekaru da dama ana yi.”

Ya kara da cewa: Har yanzu akwai dubban masu fafutuka daga Hamas da sauran kungiyoyi a zirin Gaza.

Ya shaida wa gidan talabijin na Channel 13 cewa: “Wadannan kungiyoyi suna karuwa kuma suna canzawa a kowane lokaci.

Da yake magana game da Hamas, ya kara da cewa: An gina mafi yawan karfin Hamas a lokacin da Sinwar yake tsarea  gidan kason Isra’ila, saboda haka koda babu Sinwar Hamas za ta ci gaba da wanzuwa kuma za ta kara karfi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments