Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Ya Zargi Isra’ila Da Neman Kunna Wutar Rikici

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana kokarin janyo Iran cikin yaki Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya ya bayyana cewa: Gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tana kokarin janyo Iran cikin yaki

Ministan harkokin wajen kasar Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana cewa: Munanan halayen haramtacciyar kasar Isra’ila sun tilastawa Iran daukar matakan da suka dace don mayar da martani, yana mai jaddada cewa haramtacciyar kasar Isra’ila tana kokarin janyo Iran cikin yaki.

Fidan ya kara da cewa – a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa da takwaransa na Iran Abbas Araqchi a birnin Istanbul – Fira Ministan gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila Benjamin Netanyahu a kullum yana kunna sabbin rikice-rikice a yankin. Fidan ya jaddada cewa bai kamata a yi sakaci da hadarin ganin yaki ya bazu a yankin Gabas ta Tsakiya gaba daya ba.

A nasa bangaren, ministan harkokin wajen Iran ya yi Allah wadai da laifukan yaki da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila take aikatawa, yana mai jaddada cewa, har yanzu akwai yiwuwar fadada yakin a yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments