Erdogan : ‘Ya Kamata A Daina Kisan Kare Dangi A Gaza Da Lebanon :

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bukaci kasashen duniya da su matsa wa Isra’ila lamba wajen kawo karshen abin da ya kira kisan kiyashin

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bukaci kasashen duniya da su matsa wa Isra’ila lamba wajen kawo karshen abin da ya kira kisan kiyashin da ta ke yi a Gaza da Lebanon.

Mista Erdogan ya bayyana hakan ne a wani taron manema labarai da shugaban kasar Jamus Olaf Scholz da ke ziyara a kasar.

A lokacin da yake jawabi a Istanbul, Erdogan ya ce shugabannin biyu sun tattauna kan “yakin kisan kare dangi da Isra’ila ke yi a Gaza da kuma hare-haren da take kai wa Lebanon dama mummunan yanayin jin kai da yankin ke ciki.

Turkiyya ta bukaci a tsagaita bude wuta cikin gaggawa tare da shigar da kayan agaji zuwa yankin, in ji Erdogan.

Matukar ana ci gaba da gudanar da wannan kisan kare dangi, to yankinmu ba zai iya samun zaman lafiya da kwanciyar hankali ba,” in ji shi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments