EU Tayi Kira Da A Tsagaita Wuta Bayan Mutuwar Sinwar

Babban jami’in kula da harkokin jin kai na Tarayyar Turai ya ce tsagaita bude wuta shi ne abun da ya kamata a fifita a rikice-rikicen

Babban jami’in kula da harkokin jin kai na Tarayyar Turai ya ce tsagaita bude wuta shi ne abun da ya kamata a fifita a rikice-rikicen dake faruwa a yankin, kuma kashe shugaban Hamas Yahya Sinwar da sojojin Isra’ila suka yi zai iya kara samun damar cimma hakan.

Babban jami’in na EU Josep Borrell ya shaida wa manema labarai cewa, an shiga wani sabon babi bayan kisan Sinwar, kuma dole ne mu yi amfani da shi wajen cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta, da sako sauran mutanen Isra’ila da aka yi garkuwa da su da kuma neman hanyar siyasa.

Har ila yau ya ce za a iya karfafa aikin wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a kasar Labanon da aka fi sani da UNIFIL.

“Dole ne a mutunta sojojin Majalisar Dinkin Duniya a duk fadin duniya… watakila dole ne a sake duba aikin UNIFIL amma abu na farko da za a yi shi ne tsagaita wuta,” in ji Borrell, yana mai cewa kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya zai yanke shawara kan batun tawagar taUNIFIL.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments