Sojojin HKI Sun CI Gaba Da Kai Hare Hare Kan Kudancin Kasar Lebanon Suna Kashe Fararen Hula

Jiragen yakin HKI suna ci gaba da kai hare hare babu kakkaunata a kan garuruwa a kudacin kasar Lebanon. Kamfanin dillancinlabaran IP na kasar Iran

Jiragen yakin HKI suna ci gaba da kai hare hare babu kakkaunata a kan garuruwa a kudacin kasar Lebanon.

Kamfanin dillancinlabaran IP na kasar Iran ya bayyana cewa a jiya Alhamis ce jiragen yakin HKI suka kai hare hare kan gidajen mutane, da kuma gine ginen gwamnati a garuruwan Kafrerman, Al-Haush, Kaouthariyet, El Saiyad, Tebnine, Tayr Harfa da Wadi al Hajir na kasar Lebanon.

Labarin ya kara da cewa, tun ranar 27 ga watan Satumba na wannan shikara ne sojojin yahudawan suke kokarin kutsawa cikin kasar Lebanon daga kudanci da kuma gabacin kasar amma suka kasa yin hakan saboda turjiyar da dakarun Hizbullah suke nunawa a kan iyakokin kasar da kasar Falasdinu da aka mamaye.

Ya zuwa yanzu dakarun hizbulla sun wargaza tankunan yaki samfurin mirkava na HKI har 17 a kan iyakokin kasashen biyu, sannan sun halaka ko kuma sun jikada daruruwan yahudawan sahyoniyya tun lokacin.

Sai dai sojojin yahudawan basa da wata hanya sai kashe fararen hula a hare haren da suke kaiwa ta sama a garuruwa da birane na kudancin kasar ta Lebanon.

A wani labarin kuma kungiyar Hizbullah ta bada sanarwan shiga ta shiga sabuwar marhala ta fafatawa da sojojin HKI, wato zasu kara yawa da kuma karfin hare haren da suke kaiwa HKI daga ranar 1 ga watan Octoban da muke ciki. Wannan bayan suka halaka sojojin HKI 55 sannan wasu kimani 500 suka ji rauni tun lokacin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments