Najeriya: Rabadu Ya Ce Wasu Makaman Da Suke Hannun Yan Ta’adda A Kasar Na Gwamnatin Kasar Ne

Mai bawa shugaban tarayyar Najeriya shawara a kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya bayyana cewa da dama daga cikin makaman da suke hannun yan ta’adda

Mai bawa shugaban tarayyar Najeriya shawara a kan harkokin tsaro Nuhu Ribadu ya bayyana cewa da dama daga cikin makaman da suke hannun yan ta’adda yan fashi da makami a kasar na gwamnatin tarayyar kasar ne.

Kamfanin dillancin labaran NAN na Najeriya ya nakalto Ribadu na fadar haka a jiya Alhamis a wani taro na yaki da yaduwar kananan makamai a hannun mutane wadanda ba jami’an tsaro ba a kasar.

Ribadu ya kara da cewa mafi munin mutane a wajensa, su ne Jami’an tsaron kasar wadanda suke saida ko kuma su bada hayar makaman da gwamnatin tarayya ta basu ga wadanda zasu dawo su kashesu ko su kashe abokan aikinsu da wadannan makamai daga baya.

Mai bawa shugaban kasa shawara ya kara da cewa, dole a tashi tsaye don karbo wadannan makamai daga hannun wadannan ashararu idan ana son dawo da  zaman lafiya mai dorewa a kasar. Ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya tana da shirye shirye don haka.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments