Shugaban Ansarullah Amurka Na Da Hannu A Duk Ta’asar ‘Yan Sahayoniyya A Gaza

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana cewa: Amurka cikakkiyar abokiyar tarayyar gwamnatin Isra’ila ce wajen aikata laifuka da wuce gona da iri kan

Shugaban kungiyar Ansarullah ta kasar Yemen ya bayyana cewa: Amurka cikakkiyar abokiyar tarayyar gwamnatin Isra’ila ce wajen aikata laifuka da wuce gona da iri kan Gaza

Shugaban kungiyar Ansarullahi ta kasar Yemen, Sayyid Abdul-Malik Badruddeen al-Houthi ya bayyana cewa: Amurka ta yi tarayya da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ‘yar mamaya ta kowace fuska tare da tafka ayyukan laifukan wuce gona da iri da zalunci kan al’ummar Falasdinu, yana mai nuni da cewa ba tare da haɗin kai da goyon bayan Amurka ba, maƙiya yahudawan sahayoniyya ba za su iya ci gaba a duk tsawon wannan lokaci da irin wannan ayyukan zalunci da muggan ayyukan wuce gona da iri kan Falasdinawa ba.

A cikin jawabin da ya gabatar ta hanyar gidan talabijin a yau Alhamis, game da sabbin abubuwan da suka faru a hare-haren wuce gona da iri kan Gaza da Lebanon da kuma ci gaban yanki da na kasa da kasa, Sayyid Al-Houthi ya ce: Wuraren da aka aikata muggan laifuka a Gaza suna dauke da gamsassun dalilai kan matakin aikata laifukan yahudawan sahayoniyya, ya kara da cewa: Ba shi da amfani a yi wa fararen hula jawabi don kare su daga abokan gaba na yahudawan sahayoniyya, kamar yadda makiya ‘yan sahayoniyya suke kai hare-hare kan ‘yan jarida, likitoci, wuraren sayar da magunguna, da malamai da dalibai da kuma dukkanin al’umma.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments