Amurka Da Burtaniya Sun Kai Hari Kan Babban Birnin Kasar Yemen

Jiragen yakin Amurka da na Birtaniya sun yi ruwan bama-bamai a birnin San’a na kasar Yeman da wasu yankuna da dama. Tashar talabijin ta al-Masirah

Jiragen yakin Amurka da na Birtaniya sun yi ruwan bama-bamai a birnin San’a na kasar Yeman da wasu yankuna da dama.

Tashar talabijin ta al-Masirah ta kasar Yemen ta bayyana cewa, hare-haren wuce gona da irin na Amurka da Birtaniya an kai su ne kan yankunan al-Hafa da Jirban da ke arewaci da kudancin babban birnin kasar a wayewar safiyar yau Alhamis.

Gidan talabijin din ya kuma ce jiragen yakin sun kai hari a yankin Sa’ada da ke arewa maso yammacin Yeman da kuma yankunan Kahlan da al-Abla da ke gabashin birnin.

Kamfanin dillancin labaran iqna ya habarta cewa, sojojin Amurka sun yi amfani da jirgin mai harba bama-bamai samfarin B-2 a karon farko a hare-hare ta sama kan kasar Yemen.

Kamfanin dillancin labaran Saba Net na kasar Yemen ya bayar da rahoton cewa, jiragen yakin Amurka da Birtaniya sun kaddamar da hare-hare har sau 15 a babban birnin kasar Sana’a da lardin Sa’ada.

ataimakin ministan yada labarai na gwamnatin San’a, Nasreddin Amer, ya yi tir da hare-haren wuce gona da iri na Amurka da Birtaniya, yana mai cewa, “Matsayin al’ummar Yemen a kan Palastinu da Lebanon ba zai canja ba da wadannan hare-hare.”

Amer ya jaddada cewa Amurka za ta fuskanci martini kan wannan ta’addancin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments