HKI Ta Yi Kisan Kiyashi A Nabadhiyyah Da Kuma Bika A  Lebanon

Jiragen yakin HKI suna cigaba da yin kisan kiyashi a sassa daban-daban na kasar Lebanon ta hanyar kai hare-hare ta sama, inda a bayan da

Jiragen yakin HKI suna cigaba da yin kisan kiyashi a sassa daban-daban na kasar Lebanon ta hanyar kai hare-hare ta sama, inda a bayan da su ka kashe mutane 16 a garuruwan kudancin kasar da kuma yankin Bika.

Bugu da kari jiragen yakin HKI sun kai wasu jerin hare-haren a unguwar Dhahiya dake cikin birnin Beirut.

A hare-haren da su ka kai a jiya a kudancin Lebanon, mutane 16 ne su ka yi shahada, daga cikinsu har da mai garin Nabadhiyyah, wasu mutanen su 52 kuma su ka jikkata.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta Lebanon wacce ta fitar da wadannan alkaluman ta kuma kara da cewa; Jiragen na HKI sun kai hari akan wani gida a garin Habush dake gundumar Nabadhiyyah.

 A tsawon ranar jiya har zuwa dare, jiragen yakin HKI sun yi ta ruwan wuta akan  garin “Aytas-sha’ab” , haka nan kuma wani harin a garin Sur.

 A yankin Bika An sami shahidai 8 sai kuma wasu fiye da 30 da su ka jikkata.

Tashar talbijin din ‘almayadin’ ta bayar da labarin cewa; a garin Yamunah, an sami shahidai 15 yayin da wasu 9 su ka jikkata.

A yammacin garin Ba’alabak kuwa wasu mutane 6 ne su ka jikkata sanadiyyar harin da jiragen yakin HKI su ka kai.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments