Ministocin harkokin wajen Iran da Faransa sun tattauna batun ayyukan yakin Isra’ila a Lebanon

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot, a wata tattaunawa ta wayar tarho, sun tattauna batutuwan da suka shafi halin

Ministan harkokin wajen Iran Abbas Araghchi da takwaransa na Faransa Jean-Noel Barrot, a wata tattaunawa ta wayar tarho, sun tattauna batutuwan da suka shafi halin da ake ciki a yankin gabas ta tsakiya,  ciki har da hare-haren da Isra’ila ke kai wa Lebanon.

Babban jami’in diflomasiyyar na Iran ya jaddada bukatar kawo karshen hare-haren da Isra’ila ke kai wa kasar Labanon, inda ya yi kira da a kawar da cikas da gwamnatin Haramtacciyar Kasar Isra’ila take haifarwa ga ayyukan agaji da na jin kai na kasa da kasa ga ‘yan gudun hijira da ke cikin  mawuyacin hali .

Ya kuma yi gargadi kan duk wani sabon yunkuri na gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila a yankin, a daidai lokacin da Tel Aviv ke ci gaba da zaluntar kasar Labanon da al’ummar zirin Gaza.

Isra’ila ta kara zafafa hare-haren da take kaiwa Lebanon bayan kaddamar da yakin kisan kare dangi a zirin Gaza a ranar 7 ga watan Oktoban bara.

Adadin wadanda suka yi shahada sakamakon hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kai wa kan Lebanon tun shekarar da ta gabata ya kai 2,350, in ji ma’aikatar lafiya ta Lebanon a wannan  Talata.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments