Isra’ila Na Ci Gaba Da Yin Fatali Da Kiraye-Kirayen Dakatar Da Bude Wuta

Rundunar sojin Isra’ila ta fara dakatar da jami’anta da dama da suka ce za su daina aikin soji da yaƙi a Gaza har sai gwamnati

Rundunar sojin Isra’ila ta fara dakatar da jami’anta da dama da suka ce za su daina aikin soji da yaƙi a Gaza har sai gwamnati ta amince da yarjejeniyar musayar fursunoni don dawo da Isra’ilawar da aka yi garkuwa da su gida.

“Dakatar da sojojin, ciki har da manya biyar da ke matsayin jiran ko-ta-kwana, ta fara ne a ‘yan kwanakin nan ta hanyar kiran waya ga dukkan waɗanda suka sanya hannu a madadinsu – ciki har da kiran da aka yi wa sojan da ke aiki a Gaza,” in ji jaridar Haaretz a ranar Talata.

“Daya daga cikin waɗanda suka sanya hannun ya faɗa wa wani soja cewa manyansa sun nemi ya sanya hannu a wasiƙar, amma ya ƙi yin hakan,” in ji jaridar.

Wani soja kuma ya bayyana kiran wayar da ‘barazana’, inda wani kuma ya ce kwamandan bataliyarsu ne ya yi kiran waya mai tsayi, wanda hakan ya janyo aka dakatar da shi, in ji jaridar.

Rahoton na Haaretz ya ƙara da cewa a makon jiya ne sojoji 130 suka sanya hannu kan wata wasiƙa inda suka sha alwashin ba za su ci gaba da aikin soji ba har sai gwamnati ta amince da tsagaita wuta a Gaza tare da tabbatar da an yi musayar fursunonin da ke tsare.

An rubuta wasiƙar ga Firaminista Netanyahu, ministoci, da shugaban rundunar soji Herzi Halevi.

Isra’ila ta yi ƙiyasin akwai mutanenta 101 da ake tsare da su a Gaza, inda Hamas kuma ta ce an kashe mutanen a hare-haren kan mai-uwa-da-wabi da Isra’ila ta kai yankin.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments