Amurka Zata Karfafa HKI Da Tsarin THAAD Na Tsaron Sararin Samaniyar Kasar

Kafafen yada labarai na HKI sun bada rahoton cewa gwamnatin Amurka za ta mikawa HKI garkuwan makamai masu linzami samfurin THAAD nan ba da dadewa

Kafafen yada labarai na HKI sun bada rahoton cewa gwamnatin Amurka za ta mikawa HKI garkuwan makamai masu linzami samfurin THAAD nan ba da dadewa ba, don tallafa mata a kan kyautata tsaron sararin samaniyar kasar.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Jami’an gwamnatin Amurka suna fadar haka ga jaridar ‘”The Times of Israel”. Sun kuma kara da cewa gwamnatin shugaba Biden ta amince da hakan, ta kuma kara da cewa tsarin tsaron sararin samaniya na THAAD zai bada garkuwan sararin samaniya HKI mai kyau daga makamai masu linzami na kasar Iran da sauran makaman makiyanta.

Kafin haka dai gwamnatin shugaba Biden ta so ta aika tsarin tsaron na THAAD don tsaron sararin samaniya tun kafin hare haren da Iran ta kai kan HKI a ranar 1 ga watan Octoban da muke ciki.

Sai dai wata majiyar ta kara da cewa HKI ta na da wannan tsarin tsaron tun shekara ta 1997, ammam ba sa aiki kamar yadda ya dace. Banda haka wannan sabon tsarin da Amurka za ta mika HKI,  Amurkawa ne za su sarrafasu don kakkabo makaman.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments