Kungiyar NLC Ta Caccaki Tinubu Kan Batun Farashin Man Fetur A Najeriya

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta caccaki Gwamnatin Bola Tinubu kan karin farashin litar man fetur da aka yi a kasar yau Laraba. Shugaban NLC

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya (NLC) ta caccaki Gwamnatin Bola Tinubu kan karin farashin litar man fetur da aka yi a kasar yau Laraba.

Shugaban NLC na kasa, Kwamared Joe Ajaero ne ya bayyana kaduwar kungiyar cikin wata sanarwa da ya fitar a yammacin wannan Larabar.

A cikin sanarwar,  Kwamared Ajaero ya ce “da alama dai babu abin da wannan gwamnatin ta sani face kara kudin man fetur ba tare da tuntubar kowa ba, ba kuma tare da an wadata ’yan kasar da hanyoyin rage radadi ba.”

Sanarwar ta ci gaba da cewa tsame hannun dillanci da kamfanin mai na kasa NNPCL ya yi tsakanin ’yan kasuwa da Matatar Dangote abin dubawa ne.

“Ya kamata gwamnati ta sake nazari ta kuma gabatar mana shirin da take yi na bunkasa tattalin arzikin Najeriya, da ci gaban kasa maimakon daukar matakan da ba su wani tasiri sai dagula lamurra,” in ji NLC.

A ranar Laraba ne aka wayi gari kamfani NNPCL ya kara farashin man a karo a biyu cikin wata guda.

A Abuja, babban birnin kasar, sabon farashin lita daya ya fara daga naira 1,030, sabanin yadda ake sayar da shi a baya kan naira 897.

A bayanan sabon farashin da NNPCL ya fitar, za a riƙa sayar da duk litar man fetur kan Naira 1,025 a gidajen mansa da ke Kudu maso Yamma sannan a riƙa sayarwa kan Naira 1,045 a Kudu maso Gabashin Nijeriya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments