Jaridar Telegraph Ta Bayyana Karfin Iran Na Kutsawa Cikin Tsaron Sararin Samaniyyar Isra’ila  

Jaridar ‘The Telegraph’ ta kasar Birtaniya ta bayyana cewa: Iran ta tabbatar da karfin ikonta na kutsawa mafi girman tsarin tsaron sararin samaniyyar duniya Martanin

Jaridar ‘The Telegraph’ ta kasar Birtaniya ta bayyana cewa: Iran ta tabbatar da karfin ikonta na kutsawa mafi girman tsarin tsaron sararin samaniyyar duniya

Martanin Iran kan haramtacciyar kasar Isra’ila ya bayyana gibi har ma fallasa raunin tsarin tsaron sararin samaniyar haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma masana sun yi gargadin yiwuwar karin rudani daga bangaren gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da zai iya haifar da babbar barna idan aka ci gaba da rikicin.

Da farko dai gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke mamaye da kasar Falasdinu ta gwada rashin muhimmancin irin barnar da harin Iran ya haifar mata, amma bisa ga abin da jaridar “The Telegraph” ta kasar Birtaniya ta ruwaito ta ce: Bayan mako guda ta bayyana cewa yana daya daga cikin hare-hare mafi muni a tarihi, harin da Iran ta kaddamar da makamai masu linzami na ballistic kan haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma harin ya yi cikakken tasiri kamar yadda a halin yanzu ya fito fili, musamman tun bayan da gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila ta yi furuci da cewa: Tabbas harin ya tarwatsa da dama daga cikin muhimman sansanonin sojinta.

Jaridar Telegraph ta ce: Iran ta tabbatar da karfin ikonta na yin kutse a tsarin tsaron sararin samaniya mafi girma a duniya. Kuma abin da zai biyo baya nan gaba, na iya zama mai muni, yayin da duniya ta kalli abin da ya faru a jajiberen shigan watan Oktoba a sararin samaniyyar haramtacciyar kasar Isra’ila, kuma aka fara yin rubutu bayan da makami mai linzamin Iran ya kutsa cikin babban na’urar tsaron yahudawan sahayoniyya na Iron Dome, duk da masaniyar cewa makaman sun tunkaro haramtacciyar kasar ta Isra’ila.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments