Kungiyar Kare Hakkin Dan Adam Ta Euro-Mediterranean Ta Yi Gargadin Kisan Kiyashi A Gaza

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Euro-Mediterranean ta buƙaci gaggata shiga tsakani don hana kisan kiyashi mafi muni a Gaza Majiyoyin kiwon lafiya sun bayyana

Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Euro-Mediterranean ta buƙaci gaggata shiga tsakani don hana kisan kiyashi mafi muni a Gaza

Majiyoyin kiwon lafiya sun bayyana cewa: Falasdinawa 43 suka yi shahada a hare-haren da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a yankuna daban-daban na Zirin Gaza tun daga wayewar garin ranar Talata, kuma ofishin yada labaran gwamnati a Gaza ya yi gargadi kan sake maimaita yanayin rugujewar rukunin kiwon lafiya a asibitin Shifa, tare da jaddada kin amincewa da aniyar ‘yan mamaya na barazanar sake mamaye asibitoci.

Sojojin gwamnatin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suna ci gaba da aikata laifin kisan kiyashi a yankin Zirin Gaza ta hanyar kai hare-hare ta sama da kuma luguden wuta ta kasa da manyan bindigogin lamarin da ke cigaba da janyo shahadan Falasdinawa tare da jikkata wani adadi mai yawa musamman a hare-haren da suka kai kan wasu yankuna na tsakiya da arewacin Zirin Gaza.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments