Sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila Sun Kai Hari Kan Kudancin Kasar Lebanon

Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai wani sabon hari kan yankin kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki

Sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai wani sabon hari kan yankin kudancin birnin Beirut na kasar Lebanon

Sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila sun kai farmaki kan wasu yankunan kudancin birnin Beirut fadar mulkin  kasar Lebanon a yammacin jiya Lahadi, biyo bayan gargadin da kakakin rundunar sojin ‘yan mamaya Avichay Adraee ya yi na ficewa daga yankunan.

Jiragen saman yakin sojojin haramtacciyar kasar ta Isra’ila sun kai farmakin ne kan wasu yankuna uku a kudancin birnin na Beirut.

Kafin kaddamar da hare-haren, a cikin gargadin kakakin rundunar sojin mamayar Avichai Adraee ya yi gargadin cewa: Jama’a su fice daga yankunan Hadath da Burj al-Barajneh, bisa da’awar akwai cibiyoyi kayayyakin muradun kungiyar Hizbullah a cikinsu, sanarwar da ke matsayin da’awar kare matakin kai hare-hare kan yankunan fararen hula.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments