Dakarun Hizbullah Na Kasar Lebanon Suna Cigaba Da Kashe Sojojin HKI

Kwanaki biyar daga kokarin yin kuste cikin kasar Lebanon, har yanzu sojojin mamayar HKI ba su iya shiga da kama wani yanki na kudancin kasar

Kwanaki biyar daga kokarin yin kuste cikin kasar Lebanon, har yanzu sojojin mamayar HKI ba su iya shiga da kama wani yanki na kudancin kasar ba, saboda turjiyar da suke fuskanta daga mayakan Hizbullah.

Majiyar dakarun kungiyar ta Hizbullah ta tabbatar da cewa a cikin wadannan kwanakin biyar sun kashe sojojin HKI 25 da kuma jikkata wasu 150.

Sojojin na HKI suna son yin kutse ne cikin Lebanon ta yankunan Marun-Ra’as” da Aytarun, da Yarun, sai dai har yanzu sun kasa shiga daya daga cikin wannan yankunan uku.

A ranar farko da sojojin mamayar su ka so shiga Lebanon din an kashe 8 daga cikinsu da hakan ya tilasata musu janyewa da komawa inda su ka fito. Bugu da kari a rana ta biyu, sojojin mamayar sun so shiga ta hanyar garin Udaisa, sai dai kashe musu sojoji 15 da dakarun Hizbullah su ka yi, da hakan ya sa kafafen watsa labarunsu bayyana cewa, suna fuskantar yanayi mai hatsarin gaske a kudancin Lebanon.

A yau Lahadi ma makamai masu linzamin da dakarun Hizbullah su ka harba cikin Falasdinu dake karkashin mamaya, sun tilasta wa  dubban ‘yan share wuri zauna a garuruwan Haifa, da Khudairah shiga karkashin kasa domin buya.

Hakan ya kara yawan wadanda su ke barin gidajensu akasin manufar yakin da Benjemine Netenyahu ya bayyana ta mayar da ‘yan share wuri zauna a Arewacin HKI gida, bayan da hare-haren kungiyar Hizbullah na tsawon shekara daya ta mayar da su ‘yan hijira.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments