Hezbollah ta kai hari kan kamfanin Elta mai kera na’urorin ayyukan soji na Isra’ila

Hezbollah na ci gaba da gwabzawa da dakarun Isra’ila da ke yunkurin kutsawa kauyukan kudancin Lebanon da ke kan iyaka da Falasdinu da ta mamaye.

Hezbollah na ci gaba da gwabzawa da dakarun Isra’ila da ke yunkurin kutsawa kauyukan kudancin Lebanon da ke kan iyaka da Falasdinu da ta mamaye.

Hizbullah ta ci gaba da kai hari kan tarukan sojojin mamaya, wuraren aiki, da matsugunansu da makaman roka.

Mayakan Hezbollah sun kai hari a kan wata cibiyar majalisar dokokin Isra’ila da ke mashigar Jal al-Deir, dake kan iyakar Lebanon da Falasdinu, tare da harba makamin  roka a kanta da misalin karfe 8:30 na dare.

Har ila yau mayakan an Hizbullah sun kai hari kan wuraren taro na Isra’ila da ke kusa da matsugunan yahudawa da ke arewacin Falasdinu da, inda suka yi amfani da wani babban makamai mai linzami wajen kai harin.

Tun da jijifin safiyar yau kungiyar Hizbullah ta kai hari kan kamfanin ELTA Systems Ltd da ke kusa da Sakhnin a gabar tekun Akka, bayan wani hari da aka kai a barikin Ma’aleh Golani da karfe 4:00 , inda mayakan an Hizbullah suka yi amfani da makaman roka.

Kamfanin Elta ya kware a bangaren ayyukan kera na’urori na ayyukan soji, wanda kuma shi ne kamfani mafi girma a cikin “Isra’ila” a bangaren wadannan ayyuka.

A halin da ake ciki kuma, kafafen yada labarai na soji sun fitar da faifan bidiyo da ke nuna harin da aka kai a yankin Krayot a gabar tekun Haifa.

Hotunan sun nuna rokokin da kungiyar Hizbullah ta harba ranar Juma’a zuwa Krayot, wani yanki mai yawan jama’a da ya kai kimanin kilomita murabba’i 20, kuma yana da tazarar kilomita 28 daga kan iyakar Lebanon da Falasdinu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments