Jagora: Kafin Isra’ila Ta Farfadon Daga Matsalar Hare-Haren ‘Yan Gwagwarmaya Za Ta Shafe Shekaru 70 Na Gaba

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Gwagwarmaya ta mayar gwamnatin ‘yan sahayoniyya baya zuwa tsawon shekaru 70 da suka gabata                               

Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran ya bayyana cewa: Gwagwarmaya ta mayar gwamnatin ‘yan sahayoniyya baya zuwa tsawon shekaru 70 da suka gabata                               

Shafin yada labarai na Jagoran juyin juya halin Musulunci na Iran Ayatullah Sayyid Ali Khamenei ya fitar da wani faifan bidiyo mai kunshe da kalaman da Jagoran juyin juya halin Musulunci ya gabatar a cikin hudubar sallar Juma’a da ya gabatar a shekaran a babban Masallacin birnin Tehran na Imam Khumaini (r.a), inda ke bayyana yadda ‘yan gwagwarmayar Musulunci suka dawo da gwamnatin ‘yan sahayoniyya baya zuwa shekaru 70 da suka gabata.

A wani bangare na wannan faifan bidiyo, Jagoran ya ce: Hakika ‘yan gwagwarmaya musamman a Gaza da Lebanon sun tilastawa makiya yahudawan sahayoniyya komawa baya a fagen shirye-shiryensu har zuwa tsawon shekaru 70 da suka gabata, wato idan har suna bukatar komawa zuwa matsayin da suke a ‘yan shekarun da suka gabata, sai sun shafe tsawon shekaru 70 suna gudanar da ayyuka ba dare ba rana kafin su dawo zuwa matsayin ci gaba da suka samu a fagen rayuwarsu.

Kamar yadda Jagoran juyin juya halin Musuluncin ya tabbatar da cewa: Al’ummar Falastinu na da cikakken ‘yancin kalubalantar wadannan makiya ‘yan mamaya, kuma babu wata kotu ko wata kungiya ta kasa da kasa da ke da hakkin yin zanga-zangar nuna adawa da matakan al’ummar Falastinu saboda gwagwarmayarsu kan ‘yan mamaya.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments