Saƙon martani mai zafi zuwa ga waɗanda suke tunanin cewa harin da Iran ta kai wa haramtacciyar kasar Isra’ila shirme ne!
Dan jaridar kasar Masar kuma mai gabatar da shirin “Masar A Yau”, Mohamed Nasir ya kalubalanci wadanda suka yi ikirarin cewa: Hare-haren makamai masu linzami da Iran ta kai kan haramtacciyar kasar Isra’ila, wani wasa ne kawai da bai shige hari kan haramtacciyar kasar Isra’ila da kayan wasan wuta na yara ba.
Hare-haren makamai masu linzami na Jamhuriyar Musulunci ta Iran sun zo ne a matsayin mayar da martani ga kisan gillar da yahudawan sahayoniyya ‘yan mamaya suka yi wa shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Isma’il Haniyeh a birnin Tehran a karshen watan Yulin wannan shekara, da kuma babban sakataren kungiyar Hizbullah Sayyid Hasan Nasrallah da kwamandan Dakarun kare juyin juya halin Musulunci, Abbas Nilforshan, a wani farmaki da sojojin gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila suka kai a kudancin birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon a ranar 27 ga watan Satumba.
Nasir ya kara da cewa a cikin shirinsa na Masar A Yau: Idan aka dauka cewa hare-haren na Iran wasa ne, to kuwa gwamnatocin Larabawa ba za su iya kai farmaki kan haramtacciyar kasar Isra’ila ba, koda ma da kayan wasan wuta na yara ne da ke tartsatsi a sama. Ya yi tambayar cewa: Shin gwamnatocin kasashen Larabawa za su iya yin wasan kwaikwayo irin na Iran?!