Janar Fadwi: Kuskuren HKI Zai Sa Mu  Kai Wa Cibiyoyinta Na Makamashi Hari

Mataimakin Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran, Janar Ali Fadwi ya bayyana cewa; Idan har HKI ta yi kuskuren kawo wa Iran

Mataimakin Kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran, Janar Ali Fadwi ya bayyana cewa; Idan har HKI ta yi kuskuren kawo wa Iran hari, to kuwa Iran din za ta kai cibiyoyinta na man fetur da Gaz, hari za kuwa ta rusa su baki daya a lokaci daya.

Janar Fadwi ya kuma kara da cewa, HKI za ta jawo wa kanta rushewa baki daya idan har ta tafka kuskuren kawo wa Iran hari.

Mataimakin kwamandan dakarun kare juyin juya halin musulunci na Iran ya fada wa tashar telbijin din ‘Almayadin” cewa; Iran kasa ce mai girma da fadi, amma HKI tana da cibiyoyin makamai guda uku ne kadai, wadanda za mu iya rusa su baki daya a lokaci daya.

Share

2 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments