Araqchi: Jamhuriyar Musulunci Ta Iran Za Ta Cigaba Da Taimaka Wa Abokanta Na Lebanon

Ministan harkokin Wajen Iran wanda ya isa kasar Lebanon, ya gabatar da taron manema labaru da a ciki ya bayyana cewa; A kodayaushe Iran tana

Ministan harkokin Wajen Iran wanda ya isa kasar Lebanon, ya gabatar da taron manema labaru da a ciki ya bayyana cewa; A kodayaushe Iran tana goyon baya da kare mutanen Lebanon, da kuma kungiyar Hizbullah,wannan ne ya sa dole mu zo Lebanon domin tattaunawa da abokanmu.”

Ministan harkokin wajen na Jamhuriyar musulunci ta Iran ya kuma kara da cewa, mun zo ne domin tabbatarwa da abokanmu cewa, muna nan a tare da su, ba za mu ja da baya ba.

Abbas Araqchi ya kuma bayyana cewa daya daga cikin manufofin zuwansa Lebanon shi ne kawo kayana taimako da agaji domin taimakwa wadanda su ka cutu daga hare-haren HKI.

Da yake amsa tambayar da aka yi masa akan me ya sa zai je Lebanon a lokacin da ake kai wa kasar hare-hare,ministan harkokin wajen na Iran ya ce; Idan ya zamana da akwai nauyi, to dole a sauke shi, kuma a bayan mun shiga cikin yanayi irin wannan a lokacin yaki.

Araqchi ya kara da cewa, a daren jiya HKI ta kai munanan hare-hare da dabbanci, da safiyar yau ma gabanin isowar jirginmu sun kai wasu hare-haren a kusa da filin saukar jirgi, amma mun saba da yanayi irin wannan,kuma azamarmu tana da karfi.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments