Dakarun Hizbullah Sun Kashe Sojojin HKI Da Dama A Yau Juma’a

A yau Juma’a dakarun Hizbullah na kasar Lebanon sun sanar da kashe sojojin HKI da dama tare da jikkata wasu a kan iyaka da Falasdinu

A yau Juma’a dakarun Hizbullah na kasar Lebanon sun sanar da kashe sojojin HKI da dama tare da jikkata wasu a kan iyaka da Falasdinu dake karkashin mamaya.

Sanarwar ta kungiyar Hizbullah ta ce mayakanta sun kai hari akan tankar yaki samfurin “Mirkava” tare da kashe wadanda suke cikinta da kuma jikkata wasu.

Har ila yau wata sanarwar ta kungiyar Hizbullah ta ce, mayakanta sun kai hari akan wata motar jigilar sojoji a kusa da garin Marun-Ra’as tare da kashe wasu, da kuma jikkata wasu.

Wata sanarwar ta kungiyar Hizbullah ta ambaci cewa; Sun kai hari da manyan bindigogi  da makamai masu linzami akan sansanonin sojan HKI dake sansanonin ‘yan share wuri zauna na “Kiryat Shimona” da “ Ruwaisatul-Alam’ dake kan tuddan “Kafar-Shuba”.

A wani gefen kafafen watsa labarun HKI sun sanar da cewa, gobara ta tashi a wurare daban-daban na yankin “Jalil’ sanadiyyar harin makamai masu linzamin da aka harbo daga Lebanon.

Wani yankin da Hizbullah ta kai wa hari, shi ne sansanin ‘yan mamaya na Sa’a-sa’a,wanda ya haddasa tashin gobara.

 Fiye da makamai masu linzami 100 ne Hizbullah ta harba wa HKI a tsawon yau Juma’a.

A daren jiya dai HKI ta harba makamai masu linzami masu yawa akan unguwar “Dhahiya” da yawansa ya kai ton 73.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments