Kasashen Cuba Da Venezuela Sun Goyi Bayan Martanin Da Iran Ta Mayarwa HKI

A ranar Talatar da ta gabata ne dai dakarun kare juyin juya halin musulunci su ka kai harin mayar da martani akan HKI da ta

A ranar Talatar da ta gabata ne dai dakarun kare juyin juya halin musulunci su ka kai harin mayar da martani akan HKI da ta yi wa shugaban kungiyar Hamas da na Hizbullah kisan gilla a Tehran da kuma Beirut.

Harin na Iran ta kai shi ne da makamai masu linzami samfura daban-daban akan muhimman cibiyoyin soja da na tsaron da suke warwatse a dukkanin fadin HKI.

Rahotannin bayan nan daga HKI sun ambaci cewa; harin na Iran ya yi barna mai yawa a cikin sansanin sojan sama na yankin Naqab.

Harin na Iran dai ya zo ne a matsayin hakkinta na mayar da martani a karkashin dokar MDD.

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Cuba ta zargi Isra’ila da hargitsa zaman lafiya a yammacin Asiya. Ta kuma bayyana cewa abinda Iran din ta yi na mayar da martani sakamako ne na wannan siyasar ta Isra’ila.

Ita ma ma’aikatar harkokin wajen Venezuella, harin Iran sakamako ne na wuce gona da irin HKI da kuma barazanar Fira minista Benjamin Netanyahu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments