Shugaban Kasar Iran Da Ya Ziyarci Kasar Qatar Ya Gana Da Shugabannin Kungiyar Hamas

A ziyarar da ya kai jiya zuwa kasar Qatar shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya gana da shugabannin kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas, inda ya

A ziyarar da ya kai jiya zuwa kasar Qatar shugaban kasar Iran Mas’ud Fizishkiyan ya gana da shugabannin kungiyar gwgawarmayar musulunci ta Hamas, inda ya tabbatar musu da cewa; Matukar HKI ta sake kai wa Iran hari, to za ta fuskanci mayar da martani mai tsananin gaske.

Shugaban na kasar Iran ya kuma ce; Kasashen yammacin turai sun yi wa Iran alkawulla na karya, su ka bukace ta da yin hakuri kar ta mayar da martani, domin za su kawo karshen yakin Gaza, amma abinda ya faru shi ne Isra’ila ta cigaba da aikata laifukan yaki, wannan ne ya tilasta mu mayar da martani mai karfi a kanta.

Shugaban na kasar Iran ya kuma ce:  Idan har Isra’ila ta tafka laifi komai karancinsa, to shakka babu za ta fuskanci mayar da martani daga sojojin Iran da karfi.

Shugaban na kasar Iran ya fada wa jami’an Hamas cewa; Kisan gillar da aka yi wa Isma’ila Haniyyah a Tehran, yana daga cikin abubuwa marasa dadi da su ka faru da shi domin ya kasance ne a ranar bikin ranstar da shi.

Har ila yau shugaban kasar na Iran wanda ya gabatar da taron manema labaru na hadin gwiwa tare da sarkin Qatar, ya kuma ce; Barkewar rikici a cikin wannan yankin ba zai yi wa turai da Amurka dadi ba ko kadan.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments