Mayakan Hizbullah Sun Halaka Sojin Isra’ila 14 A Lokacin Da Suka Kutsa Kan Iyakar Lebanon

Mayakan kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Labanon Hizbullah sun yi nasarar tunkarar rundunar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da suke yunkurin kutsawa cikin yankin na Lebanon

Mayakan kungiyar gwagwarmayar Musulunci a kasar Labanon Hizbullah sun yi nasarar tunkarar rundunar sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da suke yunkurin kutsawa cikin yankin na Lebanon ta kauyen Odaisseh daga yankin Khallet al-Mahafer a safiyar yau Laraba, kamar yadda kungiyar Hizbullah ta tabbatar.

An yi kazamin artabu, wanda ya tilastawa sojojin mamaya na Isra’ila ja da baya bayan da Hizbullah ta halaka tare da jikkata wasu daga cikinsu.

Wakilin tashar Al Mayadeen a Kudancin Lebanon ya rawaito cewa, kungiyar Hizbullah ta yi wani shiri na kwanton bauna kan wasu gungun sojojin haramtacciyar kasar Isra’ila da ke shirin kutsawa daga Odaisseh da Kfar Kila.

Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahotannin da ke cewa, dakarun yahudawa suna fuskantar yanayi mai tsanani matuka a kan iyakar Lebanon.

Haka nan nan kuma wasu shafukan yada labarai na Isra’ila sun nuna hotunan jiragen sama masu saukar angulu suna kwashe wadanda suka halaka da kuam wadanda suka jikkata a daga cikin sojojin Isra’ila da suka yi yunkurin kutsawa a cikin Labanon.

Kungiyar Hibullah ta ce har yanzu fitattun zaratan mayakan da narundunar Ridwan basu fara shiga cikin yakin ba, sanann kuma kungiyar ta yi shiri na yin yaki na dogon lokaci tare da Isra’ila.

Share

4 1 vote
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments