Makamai Masu Linzami Wadanda Kasar Iran Ta Mallaka Zasu Bawa Duniya Mamaki Idan sun Fara Amafani Da Su

Toshon kwamandan dakarun IRGC, Mohammad Esmaeil Kowsari wanda kuma dan majalisar dokoki ne na kasar Iran a halin yanzu, ya bayyana cewa Iran tana da wasu

Toshon kwamandan dakarun IRGC, Mohammad Esmaeil Kowsari wanda kuma dan majalisar dokoki ne na kasar Iran a halin yanzu, ya bayyana cewa Iran tana da wasu makamai masu Linzami wadanda har yanzun bata taba amfani da su ba kuma zasu bawa duniya mamaki.

Tashar talabijan ta Presstv a nan Tehran ta nakalto tsohon kwamandan yana fadar haka a jiya Talata bayan da dakarun IRGC suka kai hare hare a kan HKI.

Kowsari ya kara da cewa a halin yanzu an kakkafa damdamalai cilla garkuwan  makamai masu linzami a duk fadin kasar don kakkabo duk wani makamin da zai shigo kasar daga HKI ko kuma kawayenta.

A jiya Talata da dare ne dakarun IRGC suka cilla makamai masu linzami kimani 400 kan cibiyoyin tsaro na HKI.

A halin yanzu har’ila yau an rufe dukkan tashoshin jiragen sama na HKI babu tashi  ko sauka saboda halin da ake ciki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments