Mayakan Hizbullah Na Kasar Lebanon Suna Cigaba Da Kai Wa HKI Hare-hare

A jiya Lahadi dakarun na kungiyar Hizbullah sun sanar da kai hare-hare sau 11 akan cibiyoyi da sansanonin ‘yan hasayoniya mabanbanta. Wuraren da hare-haren na

A jiya Lahadi dakarun na kungiyar Hizbullah sun sanar da kai hare-hare sau 11 akan cibiyoyi da sansanonin ‘yan hasayoniya mabanbanta. Wuraren da hare-haren na kungiyar Hizbullah  su ka  shafa, sun kunshi “Ofik, “ Manara”, Sa’ir, “ Rosh Bina’ sai Shatula da Sonobar.

Bugu da kari kungiyar ta Hizbullah ta kai wasu hare-haren a sansanonin “Ramiya’ Alyatkim’ sai kuma Zofolon.

Sanarwar da kungiyar ta Hizbullah ta rika fitarwa ta ambaci cewa, tana kai wadannan hare-haren ne domin taimakawa Gaza da kuma martani akan hare-haren  da ‘yan sahayoniya suke kai wa Lebanon.

A cikin kwanaki biyu da su ka gabata, kafafen watsa labarun HKI sun ambaci cewa, daga Lebanon an harba makamai masu linzami akan gabashin Kudus da ya fada akan wani rukunin gidajen ‘yan share wuri zauna.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments