Iran Zata Karfata Dangantakarta Da Sojojin Ruwa na Kasar Chaina

Babban kwamandan sojojin ruwa na JMI Shahram Irani wanda yake ziyarar aiki a birnin Beijing na kasar Chaina tare da tawagarsa, ya bayyana cewa gwamnatin

Babban kwamandan sojojin ruwa na JMI Shahram Irani wanda yake ziyarar aiki a birnin Beijing na kasar Chaina tare da tawagarsa, ya bayyana cewa gwamnatin JMI zata kara karfafa dangantaka da sojojin ruwa na kasar Chaina, saboda kara karfin sojojin ruwan kasar da kuma musayar fasaha a tsakaninsu.

Kamfanin dillancin labaran IP na kasar Iran ya nakalto Irani yana fadar haka jim kadan bayan ganawarsa da babban kwamandan sojojin ruwa na kasar China, wanda ya gayyaceshi zuwa kasar.

Labarin ya kara da cewa Irani ta tawagarsa sun ziyarci makarantar horarta sojojin na kasar China dake birnin Beijing.

Ana saran bangarorin biyu zasu tattauna al-amuran da suka shafi aiki tare wajen horar da sojojin ruwa, ayyukan atisayen sojojin ruwa na hadin giuwa, da kuma batun samar da aminci a cikin takunan kasa da kasa har’ila yau da kuma yaki da ayyukan ta’addanci na cikin takunan kasa da kasa.

Daga karshen bangaroin biyu zasu tattauna kan al-amuran da suka shafi kasashen biyu.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments