Hezbollah ta kai hari sansanin sojin Isra’ila na Ilaniya

A ci gaba da goyon bayan al’ummar Palastinu da tsayin daka waje kare kasar Labanon da al’ummar kasar, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta sanar

A ci gaba da goyon bayan al’ummar Palastinu da tsayin daka waje kare kasar Labanon da al’ummar kasar, kungiyar gwagwarmayar Musulunci ta Hizbullah ta sanar da cewa ta kai hari kan sansanin sojojin Haramtacciyar Kasar Isra’ila na Ilaniya da ke arewacin Palastinu da yahudawa suka mamaye, inda ta yi amfani makamai mai linzamu samfurin Fadi-1.

Sansani na Ilaniya na Isra’ila yana da alaka da Runduna ta 146, da ke yankin arewacin Falastinu.

Wakilin Al Mayadeen a kudancin kasar Labanon ya rawaito cewa, Hizbullah ta harba wasu makaman masu linzami daga kasar Lebanon zuwa yankin al-Jalil panhandle da ke arewacin Palasdinu a kan dandazon sojojin yahudawa.

A cikin wannan yanayi, kafofin yada labaran Isra’ila sun ba da rahoton cewa, an yi ta jin karar harbe-harbe ta sama a matsugunnan yahudawa da ke yankunan Kiryat Shmona, Kfar Giladi, da Kfar Yuval, da kuma tuddan Golan na Syria da Isra’ila ta mamaye, inda ake zaton cewa kungiyar Hizbullah c eta kai hare-hare a yankunan da jiragen yaki marasa matuki.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments