Iran: Pezeshkian Zai Halarci Taron Koli Na BRICS Da Za A Gudanar A Rasha

Jakadan kasar Iran a kasar Rasha ya ce shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Masoud Pezeshkian zai halarci taron kungiyar kasashe masu tasowa ta BRICS mai

Jakadan kasar Iran a kasar Rasha ya ce shugaban Jamhuriyar Musulunci ta Iran Masoud Pezeshkian zai halarci taron kungiyar kasashe masu tasowa ta BRICS mai zuwa, wanda aka shirya gudanarwa a birnin Kazan na kasar Rasha a wata mai zuwa.

Kazem Jalali ya bayyana cewa, Pezeshkian zai kuma gana da takwaransa na Rasha Vladimir Putin a ziyarar da zai kai Kazan a watan Oktoba.

Birnin Kazan na yammacin kasar Rasha na shirin karbar bakuncin taron kasashen BRICS karo na 16 daga ranar 22 zuwa 24 ga watan Oktoba.

Tuni dai Putin ya ce yana shirin ganawa da kuma tattaunawa da takwaransa na Iran Masoud Pezeshkian game da shingayen taron, inda ya kara da cewa Rasha tana kuma sa ran ziyarar ta shugaba Pezeshkian za ta mayar da hankali wajen cimma yarjejeniyar hadin gwiwa ta hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu.

Shugaba Putin ya bayyana hakan ne a wata ganawa da ya yi da babban sakataren majalisar koli ta tsaron kasar Iran Ali Akbar Ahmadian a gefen taron manyan jami’an tsaro na kasashen BRICS a birnin St. Petersburg na kasar Rasha.

A ranar Talata, baitul malin Amurka da ma’aikatar harkokin wajen Amurka suka kakaba takunkumi kan mutane da hukumomi da dama da ke Iran da Rasha bisa zargin Tehran da sayar da makamai masu linzami ga Moscow.

Kasashen Jamus da Faransa da kuma Burtaniya sun kuma sanar da soke yarjejeniyoyin zirga-zirgar jiragen sama da suka kulla da Iran tare da yin aiki don kakaba takunkumi kankamfanin zirga-zirgar jiragen sama na kasar Iran.

Iran ta yi watsi da zargin mika wa Rasha makamai masu linzami da cewa ba shi da tushe ballantana makama.

Kazalika Moscow ta yi watsi da rahotannin kafafen yada labaran Amurka da ke cewa Iran ta aike da makamai masu linzami masu cin gajeren zango zuwa Rasha domin a yi amfani da su a yakin Ukraine.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments