Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta bada sanarwan kai hare hare kan sojojin HKI a yankin Galili na arewacin kasar Falasdinu da aka mamaye tare da amfani da makamai masu linzami samfurin katusha da kuma jiragen yaki masu kunan bakin waje wato ‘drones’.
Majiyar kafafen yada labarai na HKI sun tabbatara da labarin faduwar makaman kungiyar Hizbullah a kan sansanin sojoji mai suna ‘Nahal Gershom’. Sannan Hizbullah ta kara da cewa hare haren na jiya jumma’a dai sun kai su ne saboda maida martani ga hare hare irinsu wadanda sojojin HKI suka kai kan wasu garuruwa a kudancin kasar Lebanon. Da kuma don tallagawa Falasdinawa wadanda suke fafatawa da sojojin HKI a gaza kimani watanni 11 da suka gabata.
Kungiyar har’ila yau ta bayyana cewa ta wargaza wata tankar yaki samfurin Merkava wanda yake tafiya kan titin Ruwaisat al-Alam-Zebdine a cikin kasar Falasdinu da aka mamaye, kuma sun wargaza shi.
Labarin ya kara da cewa, dakarun Hizbullah sun kai wasu hare haren kan barikin sojoji na Zebdine da ke kan tuddan gonakin Sheb’aa na kasar Lebanon da aka mamaye.