Gaza: Kungiyar Jihadul Islami Ta Fallasa Asirin HKI Na Kokarin Ware Kungiyar Hamas A Musayar Fursinoni

Mataimakin shugaban kungiyar Jihadul Islami daya daga cikin kungiyoyi masu gwagwarmaya da sojojin HKI a Gaza, da sauran yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Muhammad Al-hindi

Mataimakin shugaban kungiyar Jihadul Islami daya daga cikin kungiyoyi masu gwagwarmaya da sojojin HKI a Gaza, da sauran yankunan Falasdinawa da aka mamaye, Muhammad Al-hindi ya ce gwamnatin HKI ta aika wakilanta guda biyu zuwa ga shuwagabannin kungiyarsa don tattauna batun musayar Fursinoni a tsakaninsu ba tare da kungiyar Hamas ba.

Tashar talabijin ta Al-Alam a nan Tehran ta nakalto Alhindi yana cewa, wani jami’in MDD ne HKI ta aika da farko don isar da wannan sakon ga kungiyar, sannan ta sake aika wani daga cikin jami’an gwamnatin kasashen yankin da sako iri guda.

Al-hindi ya kammala da cewa kungiyar ta maida martani da cewa ba zata taba kulla wata yarjeniya da HKI ba tare da kungiyar Hamas ba.

 

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments