Majalisar Dinkin Duniya Ta Yi Tofin Allah Tsine Kan Shirin Korar Falasdinawa Daga Garuruwansu

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da kalaman ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila kan batun Gabar yammacin kogin Jordan Majalisar Dinkin Duniya ta

Majalisar Dinkin Duniya ta yi Allah wadai da kalaman ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila kan batun Gabar yammacin kogin Jordan

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kakkausar suka ga kalaman ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila Yisrael Katz, wanda ya sha alwashin daukan matakin korar Falasdinawa na wucin gadi daga garuruwan Jenin da Tulkarm da ke yankin gabar yammacin kogin Jordan da aka mamaye.

Mai magana da yawun ofishin kare hakkin bil adama ta Majalisar Dinkin Duniya Ravina Shamdasani ta bayyana a yau Juma’a daga birnin Geneva cewa: “Wadannan kalamai na ministan harkokin wajen haramtacciyar kasar Isra’ila suna kara ta’azzara mummunan yanayi ne kawai, tana mai jaddada cewa furta irin wadannan kalamai daga jami’ai na iya karfafa keta hakkin bil’adama.

Jami’ar Majalisar Dinkin Duniyar ta bayyana matukar damuwarta game da abin da ke faruwa a Gabar Yammacin Kogin Jordan, inda sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka kaddamar da hare-haren wuce gona da iri, tare da gargadin hadarin da ke tattare da ta’azzara lamarin.

Tun a ranar Larabar da ta gabata ce, sojojin mamayar haramtacciyar kasar Isra’ila suka fara kai farmakin soji a arewacin gabar yammacin kogin Jordan, wanda shi ne mafi girma tun shekara ta 2002, wanda ya yi sanadin shahada da raunata Falasdinawa masu yawa.

Share

0 0 votes
Article Rating
Subscribe
Notify of
0 Comments
Oldest
Newest Most Voted
Inline Feedbacks
View all comments