Ƙungiyar haɗin kan ƙasashen yakin Sahel (AES) mai mambobi uku – Mali da Nijar da Burkina Faso – da ke ƙarƙashin mulkin soja sun ɗorawa sauran kasashen kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka haraji na kayakin da suke shigowa kasashen uku.
Jaridar Premium Time Hausa ta kara da cewa Sahel ta sanya haraji na 0.5% kan dukkan kayan da za a shigo da su ƙasashensu, daga ƙasashe da suke mambobin ƙungiyar raya tattalin arziƙi na yammacin Afirka (ECOWAS).
A cikin wata sanarwa haɗin guiwa a makon da ya gabata, ƙungiyar AES ta ce tana son amfani da kudaden ne don tafiyar da al-amuran ƙungiyar.
Harajin, wanda ya fara aiki daga ranar Juma’ar da ta gabata zai shafi duk wani kaya da za a shigo da su daga ƙasashen da ke cikin ƙungiyar ECOWAS da za su shigo ƙasashen uku.
Wannan sabuwar doka dai, ta ci karo da yunƙurin da ƙungiyar ECOWAS ke yi na bai wa ƙasashen da ke ƙungiyarta da ma ta AES damar shigar da kaya ba tare da shinge ba, duk kuwa da ficewar ƙasashen uku daga ƙungiyar a watan Janairun da ya gabata.
ECOWAS dai ta tabbatar da ci gaba da ba wa, kayakin da ake shigo da su daga ƙasashen uku damar wucewa ba tare da shinge ba kamar yadda tsarin cinikayya da zuba jari na ƙungiyar (ETLS) ya tanada.