Girgizan Kasa Mai Karfin Ma’aunin Richter 6.8 Ta Aukawa Kasashen Peru Ekwado, Mutane Akalla 14 Sun Rasa Rayukansu

2023-03-19 13:04:51
Girgizan Kasa Mai Karfin Ma’aunin Richter 6.8 Ta Aukawa Kasashen Peru Ekwado, Mutane Akalla 14 Sun Rasa Rayukansu

Majiyar fadar shugaban kasar Ecuador ta bada sanarwar cewa akalla mutane 14 suka rasa rayukansu, wasu suka ji rauni sannan wasu gine-gine suka lalace sanadiyyar wata girgizan kasa mai karfin ma’aunin Richter 6.8 da ta aukawa kasar a jiya Asabar.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta bayyana cewa jami’an bada agaji suna gaggawa don ganin sun ceto wadanda suke da sauran shan ruwa karkashin gine-ginen da suka rubta.
Cibiyar kula da al-amuran girgizan kasa ta Amurka ta bayyana cewa ta auku ne da misalign karfe 12.12 na lokacin kasashen biyu kuma tana da zurfin kilomita 66 karkashin kasa.
Labarin ya kara da cewa cibiyar girgizan kasar tana kan garin Balao dake kan iyaka da kasar Peru amma cikin kasar Ecuador.
A Peru dai hukumomin da abin ya shafa sun bayyana cewa babu wata marya mai yawa wanda girgizan kasar ta haddasa ga mutane ko kuma gine-gine. Akwai dai wadanda suka ji rauni.Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!