Najeriya: An Fara Aiki Da Sabon Shirin Ajiyar Kudade A Bankin jaiz Domin Tafiya Aikin Hajji

An fara aiwatar da wani sabon shiri da
aka bullo da shi a Najeriya na ajiyar kudade domin tafiya aikin hajji.
Shafin Nairamitrics ya bayar da
rahoton cewa, a halin yanzu an fara aiwatar da shirin karbar kudin ajiya a
bankin Jaiz da ke Najeriya, domin taimaka masu bukatar zuwa aikin hajji wajen
tara kudadensu.
Wannan shiri an fara aiwatar da shi
ne biyo bayan wani hadin gwiwa da aka yi tsakanin hukumar alhazai ta kasa da
kuma bankin na Jaiz, inda a halin yanzu shirin ya fara aiki a hukumance.
Mukaddashin babban darakta na bankin
Jaiz a Najeriya Isma’il Adamu ya bayyana wannan shiri da cewa, yana daya daga
cikin muhimman ayyuka da bankin ya kirkiro a najeriya, wadanda za su taimaka ma
musulmi masu son tafiya aikin hajji, musamman marasa karfi daga cikinsu.
Ya ce yanayin tsarin a jiyar kudden yana a matakai daban-daban ne, akwai mataki na gajeren zango, akwai mataki na matsakaicin zango, akwai kuma mataki na dogon zango, wanda mutum yana da zabin daukar kowane mataki yake bukata daidai karfinsa.
015