​Allah Ya Yi Wa Fitaccen Dan Gwagwarmaya Anis Naqqash Rasuwa

2021-02-22 20:39:57
​Allah Ya Yi Wa Fitaccen Dan Gwagwarmaya Anis Naqqash Rasuwa

A yau ne Allah ya yi wa fitaccen dan gwagwarmaya da mamayar Isra’ila a kasashen musulmi da na larabawa Anis Naqqash rasuwa.

Tashar Almayadeen ta bayar da rahoton cewa, a yau ne Allah ya yi fitaccen dan gwagwarmaya da mamayar Isra’ila a kasashen musulmi da na larabawa Anis Naqqash rasuwa a birnin Damascus na kasar Syria yana da shekaru 70 a duniya, bayan kamuwa da cutar Corona.

Anis Naqqash wanda dan kasar Lebanon, ya sadaukar da mafi yawan rayuwarsa ta kuruciya wajen gwagwarmaya da zalunci irin na Isra’ila da ma kasashe ‘yan mulkin mallaka.

Ya kasance tare da jagoran kungiyar kwatar ‘yancin kai ta Falastinawa PLO, wato marigayi malam Yasir Arafat, a cikin harkokinsa na gwagwarmaya da zalunci da kuma mamayar Isra’ila a kan yankunan Falastinu.

Baya ga haka kuma Naqqash ya kasance daga cikin mutanen ad suka kasancea sahun gaba wajen ayyukan gwagwarmayar fatattakar Isra’ila daga kasar Lebanon, inda ya kasance daga cikin masu bayar da shawarwari ga manyan kwamandojin kungiyar Hizbullah.

Anis Naqqash ya shahara a baya-bayan nan a matsayin mai sharhi kan harkokin siyasar duniya da kuma yankin gabas ta tsakiya a manyan kafofin yada labarai na kasashen larabawa.

A gobe ne za a gudanar da janazarsa a birnin Beirut fadar mulkin kasar Lebanon.


015

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!