Iran Zata Dakatar Da Hadin Kan Da Take Bawa Hukumar IAEA Dangane Da Shirinta Na Makamashin Nukliya

2021-02-15 22:36:27
Iran Zata Dakatar Da Hadin Kan Da Take Bawa Hukumar IAEA Dangane Da Shirinta Na Makamashin Nukliya

Gwamnatin kasar Iran ta bada sanarwan cewa zata dakatar da hadin kai na kari wanda ta bawa hukumar IAEA don sanya ido a shirinta na makashin Nukliya, daga ranar 21 ga watan Fabrairu da muke ciki idan sauran kasashen da suka rattabawa yarjejeniyar JCPOA basu cika alkawulanda suka dauka a cikin yarjejeniyar ba.

Tashar talabijin ta Presstv a nan Tehran ta nakalto Saeed Khadibzade kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar yana fadar haka a yau Litinin.

Khadibzade ya kara da cewa wannan yana nufin Tehran za ta dakatar da damar da ta bawa hukumar IAEA na sanya ido a kan wasu shirye-shiryenta na makashin nukliya wadanda ba wajibi ne a kanta ba bisa abinda ya hau kanta a yarjejeniyar NPT.

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar ta Iran ya kammala da cewa duk da haka Iran za ta ci gaba da kasancewa cikin yarjejenitar ta NPT da kuma ta JCPOA, kuma za ta kaiwa hukumar IAEA rahotannin ayyukanta na nukliya kamar yadda ta saba.

A shekara ta 2018 ne gwamnatin kasar Amurka ta fice daga yarjejeniyar JCPOA sannan ta dorawa Iran takunkuman tattalin arzki mafi muni a tarihin kasar.Tuni dai Jakadan Iran a hukumar IAEA ya mikawa shugaban hukumar takardan sanarwan matakin da Iran za ta dauka a ranar 21 ga wannan watan.

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!