Iran, Rasha Da China Za Su Yi Atisayen Soja A Tekun India Nan Gaba Kadan

2021-02-09 09:06:03
Iran, Rasha Da China Za Su Yi Atisayen Soja A Tekun India Nan Gaba Kadan

Kasashen Iran, Rasha Da China Za Su Yi Atisayen Soja A Tekun India Nan Gaba Kadan

Jakadan kasar Rasha a Iran, Levan Dzhagaryan ne ya sanar da cewa a tsakiyar wannan wata na Febrairu ne kasashen uku za su yi rawar daji akan tekun India.

Jakadan na Rasha ya ci gaba da cewa manufar atisayen shi ne karffa hanyoyin ceto da kuma tabbatar da tsaron sufuri a doron ruwa.

A cikin watan Disamba na 2019 ne dai kasashen uku su ka yi wani atisyaen kwatankwacin wannan.

Kafafen watsa labarun ‘yan sahayoniya sun bayyana atisayen da cewa wani yunkuri ne daga Iran domin kalubalantar jiragen ruwan kasashen turai a doron ruwa.

031

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!