Final CHAN 2020 : Morocco Da Mali Na Fafatawa A Wasan Karshe

2021-02-07 21:02:40
Final CHAN 2020 : Morocco Da Mali Na Fafatawa A Wasan Karshe

A fagen wassani, yau Lahadi kasashen Mali da Morocco, ke fafatawa a wasan karshe na gasar cin koshin kwallon kafa na ‘yan wasan dake murza leda a gida cewa da CHAN 2020, dake gudana da jamhuriyar Kamaru.

Morocco dai ita ce ke rike da kofin gasar na 2018, inda take neman sake daukan kofin a karo na biyu, yayin da Mali ke neman mallakarsa a karon farko, wanda kuma idan hakan ta tabbata shi ne zai kasance karon farko da wata kasa daga yammacin Afrika za ta dauki kofin gasar, wacce ita ce karo na shida a bana.

Idan dai Morocco ta lashe kofin shi ne karon farko da wata kasa ta dauki kofin sau biyu a jere a tarihin gasar ta CHAN.

Babu wata kasa ta yammacin AFrika da ta taba daukar kofin gasar.

A wasan neman matsayi na uku da aka buga jiya Asabar, Guinea ta lallasa Kamaru mai masaukin baki da ci (2-0), wanda ya baiwa Guinea samun matsayin na uku a gasar.

024

Comments(0)
Success!
Error! Error occured!