Chadi : Ana Zanga zangar Adawa Da Sake Tsayawa Takarar Shugaba Deby

2021-02-07 09:13:57
Chadi : Ana Zanga zangar Adawa Da Sake Tsayawa Takarar Shugaba Deby

Idriss Deby wanda ya kwashe shekaru 30 akan karagar mulki, zai sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na 6 bayan da jam’iyyar da take mulki a kasar ta sake tsayar da shi takara.

A jiya Asabar ne dai daruruwan ‘yan adawa su ka hau kan titunan birnin N’Djamem domin nuna rashin amincewarsu da sake tsayawa takarar shugaban kasar da zai ba shi damar yin wasu shekaru 7 akan karagar mulki. Masu Zanga-zangar sun kona tayoyi akan tituna suna kuma bayar da taken cewa “Ba su aminta da sake tsayawa takara karo na shida ba.”

Jami’an tsaro sun yi amfani da hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu Zanga-zanga.

A shekarar 2018 ne aka yi wa tsarin mulkin kasar ta Chadi kwaskwarima da hakan ne ya bai wa shugaban kasar damar ci gaba da yin takara ba tare da iyaka ba.

A ranar 1 ga watan Aprilu ne dai za a yi zaben shugaban kasar ta Chadi.

031

Tags:
Comments(0)
Success!
Error! Error occured!